Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afrika ta kudu ta samu karin mace mace 10 dake da alaka da COVID-19
2020-05-06 12:14:56        cri
A jiya Talata kasar Afrika ta kudu ta sanar da rahoton mutuwar mutane 10 dake da alaka da cutar COVID-19, hakan shi ya kawo adadin yawan mutanen da cutar ta kashe a kasar zuwa 148.

Cikin wadanda suka mutun, 7 daga lardin yammacin Cape ne, kamar yadda ministan lafiyar kasar Zweli Mkhize ya sana.

Ya zuwa ranar Talatar, adadin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a kasar Afrika ta kudu ya kai 7,572, adadin ya karu da 352 daga adadin ranar Litinin.

A cewar Mkhize, kawo yanzu kasar ta gudanar da aikin gwaje gwajen cutar kimanin 268,064, inda aka kammala aikin gwaje gwaje 10,523 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China