Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi kira da hadin kai da aminci tsakanin kasashe mambobin kwamitin sulhu na MDD
2020-05-16 16:20:00        cri

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira da samar da hadin kai da aminci a tsakanin kasashe mambobin kwamitin sulhu na MDD, yana mai jaddada cewa, yanzu kasashen duniya na bukatar hulda a tsakaninsu fiye da ko yaushe.

Yayin wani taro ta kafar bidiyo da aka yi jiya, Zhang Jun ya ce, ya kamata su karfafa hadin kai da aminci a tsakaninsu, tare da kulla dangantaka mai ma'ana.

Jakadan na kasar Sin, ya ce kasarsa na kira ga mambobin kwamitin sulhun su kara aminta da juna da tuntubar juna bisa adalci da sanin ya kamata da kawar da rashin yarda, tare da samar da hanya mafi karbuwa ga kowa ta warware sabani.

Dangane da batutuwan da suka shafi tsaro da zaman lafiyar kasa da kasa, Zhang Jun ya ce, kamata ya yi mambobin kwamitin su cimma matsaya guda da la'akari da bukatun dukkan bangarori da kaucewa siyasantar da batu tare da tabbatar da cewa kwamitin na taka rawar da ya kamata a lokuta masu muhimmanci.

Da yake tsokaci game da ayyukan kwamitin, Zhang Jun ya ce ya kamata su mayar da hankali kan ayyukan kwamitin na magance muhimman batutuwan dake barazana ga tsaro da zaman lafiya a duniya.

Ya ce ya kamata kwamitin ya mayar da hankali kan muhimman batutuwan da suka shafi yankuna da kasa da kasa da warware rikicin siyasa da ci gaba da ba da muhimmanci ga nahiyar Afrika.

Ya ce ya zama wajibi dagewa wajen hada hannu da sauran hukumomi domin magance tushen abubuwan dake haddasa rikici, da kuma tabbatar da samun ci gaba da hanyar wanzar da zaman lafiya, da kuma wanzar da zaman lafiya ta hanyar ci gaba.

Game da abubuwan da suka zarce hurumin kwamitin kuwa, ya ce kwamitin ya hada hannu da sauran hukumomi, kamar babban zauren MDD da hukumar kula da tattalin arziki da zamantakewa ta majalisar.

Bugu da kari, ya ce abu mafi muhimmanci a yanzu shi ne, hadin kan kasa da kasa wajen yaki da COVID-19, da mara baya ga bukatar sakatare janar na MDD ta tsagaita bude wuta da janye takunkuman da wani bangare guda ya sanya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China