Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU da MDD sun yi kira da a gudanar da zabuka cikin lumana a Burundi
2020-05-18 10:58:01        cri
Kungiyar tarayyar Afirka (AU) da MDD, sun bukaci mahukuntan kasar Burundi, da su samarwa 'yan kasar cikakken tsaro da ma yanayin da ya dace, ta yadda za su kada kuri'unsu a zabukan shugaban kasa da na kananan hukumomin kasar da aka shirya gudanarwa a ranar Laraba dake tafe.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar gabanin zabukan kasar, hukumomin sun bayyana cewa, suna sanya ido kan yakin neman zaben dake gudana, sun kuma damu kan rahotannin tsoratarwa da tashin hankali da ake samu tsakanin magoya bayan 'yan adawa"

Hukumomin AU da MDD, sun bukaci dukkan sassa da zabukan ranar 20 ga watan Mayun shekarar 2020 ya shafa, da suka hada da dakarun tsaro da kafofin watsa labaran gwamnati, da su ba da cikakkiyar gudummawa wajen samar da yanayi na zaman lafiya da tsaro, a matsayin ginshikin gudanar da zabe cikin lumana, gaskiya da zai kunshi kowa da kowa, ba tare da rufa-rufa ba, wanda kuma kowa zai lamunta a kasar ta Burundi.

Bugu da kari, sun bukaci dukkan masu ruwa da tsaki a harkokin siyasar kasar, da su guji tayar da duk wani nau'i na tashin hankali ko kalaman nuna tsana, kana su rungumi akidar tattaunawa, da za ta kai ga gudanar da zabuka cikin lumana. Haka kuma sun karfafawa hukumomin Burundin gwiwa, da su tabbatar cewa, sun baiwa mata damar shiga a dama da su yayin shirye-shiryen zaben.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China