Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zaman Karkon Tattalin Arzikin Sin Zai Ba Da Taimako Ga Bunkasuwar Tattalin Arzikin Duniya
2020-05-29 13:38:12        cri

Jiya Alhamis, an rufe taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, a yayin da yake ganawa da 'yan jaridu na kasar Sin da na kasashen ketare bayan taron, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya yi tsokaci kan harkokin dake shafar bunkasuwar tattalin arzikin Sin, karfafa hadin gwiwa da kasa da kasa da sauransu. Li Keqiang, ya nuna aniyar kasar Sin ta cimma burin bunkasuwar tattalin arzikin kasar na bana, lamarin da ya nuna, aniyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da ta gwamnatin kasar wajen tallafawa al'ummar kasa, da bada gudummawa ga farfadowar tattalin arzikin duniya.

Cikin taron manema labarai, firaminista Li Keqiang ya yi bayani kan matakan da kasar Sin ta dauka domin tabbatar da samun aikin yi ga jama'ar kasa, kyautata zaman rayuwar al'umma, da habaka kasuwanni. Lamarin da ya nuna burin shugabannin kasar Sin na kare zaman karko na tattalin arzikin kasa, da aniyarsu ta kawar da talauci baki daya a nan kasar.

Ban da haka kuma, kasar Sin ta jaddada cewa, ba za ta rufe kofarta ba, za ta ci gaba da bude kofa ga waje domin yin hadin gwiwa da kasa da kasa, Sin za ta bada gudummawa ga farfadowar tattalin arzikin duniya, a yayin da take neman bunkasa tattalin arzikinta cikin zaman karko da bude kofa ga waje.

A sa'i daya kuma, Li Keqiang ya ce, yanzu, akwai manyan kalubaloli guda biyu dake gaban gamayyar kasa da kasa, wato yaki da cutar numfashi ta COVID-19 da raya tattalin arziki, ya kamata mu hada kanmu domin cimma nasarar shawo kan wadannan kalubaloli.

Neman hadin gwiwa da cimma moriyar juna abu ne mai kyau ga dukkanin bangarori, cikin tarukan majalissun biyu na bana, gwamnatin kasar Sin ta fidda jerin matakai bisa ka'idar martabar al'umma, lamarin da ya baiwa al'ummar kasar karfin fuskantar kalubalolin dake gabansu, da baiwa kasashen duniya karfin farfado da tattalin arzikinsu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China