Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Lura Da Ka'idojin Tattalin Arziki Ya Baiwa Kasar Sin Damar Cimma Burin Raya Kanta
2020-05-22 20:01:45        cri

 

Rahoton aikin gwamnatin da firaministan kasar Sin ya kan gabatarwa taron shekara-shekara, na majalissar wakilan jama'ar kasar, ya kan nuna alkiblar da za a bi, a kokarin aiwatar da matakan raya tattalin arziki a kasar Sin.

A rahoton aikin gwamnati da firaminista Li Keqiang na kasar Sin ya gabatar a yau Juma'a, ba a tsayar da mizanin karuwar tattalin arziki da za a cimma a bana ba, maimakon haka an jaddada muhimmancin samar da isassun guraben aikin yi, da tabbatar da ingancin rayuwar jama'a, da kawar da talauci baki daya daga kasar, gami da kafa wata al'umma mai walwala.

To amma ko me ya sa ba a kayyade yawan karuwar tattalin arziki da za a nemi samu ba? Dalili a nan shi ne, ana mai da hankali sosai kan ka'idoji da tsare-tsaren tattalin arziki. Yanzu haka annobar COVID-19 na ci gaba da yaduwa a duniya, lamarin da ya haddasa koma bayan tattalin arzikin kasashe daban daban, gami da wani yanayi na rashin tabbas, musamman ma a fannonin aikin shawo kan cutar, da tattalin arziki, gami da cinikayya. Ta la'akari da wannan yanayi da ake ciki ne, gwamnatin kasar Sin ta zabi magance tabbatar da wani mizanin karuwar tattalin arzikin kasar, ta yadda za a samu damar kula da sauran ayyuka yadda ake bukata.

Idan an yi nazari kan rahoton aikin gwamnatin kasar Sin na bana, za a ga cewa, an fi mai da hankali kan fannoni 3, wato samar da guraben aikin yi, da kyautata zaman rayuwar jama'a, gami da rage talauci. Duk wadannan manufofi sun nuna yadda jam'iyya mai mulki a kasar, wato jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin take mai da hankali kan moriyar jama'a matuka. Saboda haka, wata mujallar kasar Australiya mai taken "Sharhi a fannin hada-hadar kudi" ta watsa wani sharhi cewa, gwamnatin kasar Sin ba ta bi al'adarta ta saka wani mizanin da za a cimma ba, maimakon haka ta ba ayyukan samar da guraben aikin yi, da kyautata rayuwar jama'a fifiko.

Annobar COVID-19 ta haifar da mummunar illa ga tattalin arzikin kasar Sin, sai dai a ganin gwamnatin kasar Sin wannan hasara ba wani abun da ake iya magancewa ba ne, domin kubutar da rayukan mutane shi ne abin da ya fi muhimmanci. Zuwa yanzu, kasar ta gabatar da matakai da yawa don neman sassanta radadin da ake ji sakamakon annobar.

Wadannan matakai sun hada da kara cin bashi, da rage kudin haraji da ake karba, da habaka zuba jari, da dai sauransu. Musamman ma za a dauki matakan tallafawa kamfanoni masu zaman kansu, musamman ma kanana da matsakaitan kamfanoni, domin hakan zai iya taimakawa cimma buri na samar da karin guraben aikin yi, gami da tabbatar da ingancin rayuwar jama'a. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China