Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matakan Kara Bude Kofar Kasar Sin Za Su Taimakawa Farfadowar Tattalin Arzikin Duniya
2020-05-23 21:12:57        cri

Jiya Juma'a, yayin da firaministan kasar Sin Li Keqiang ke gabatar da rahoton aikin gwamnatin kasar na shekarar 2020 ga taron shekara-shekara na majalissar wakilan jama'ar kasar, ya nanata manufar kasar ta habaka bude kofa ga kasashen waje, don neman damar zurfafa wasu gyare-gyare a kasar, tare da neman samun ci gaban tattalin arziki. Zancensa ya nuna ra'ayin gwamnatin Sin na neman samar da wani muhalli mai bangarori da yawa a duniya, wanda kuma zai karfafa zukatan mutanen duniya game da samun farfadowar tattalin arziki.

Haka zalika, cikin rahoton an tanadi matakan da za a dauka a fannonin ciniki, da amfani da jarin waje, da saukaka aikin zuba jari. Sa'an nan an jaddada niyyar kare wani tsarin ciniki da bangarorin duniya daban daban suka shiga a dama da su, gami da aiwatar da yarjejeniyar ciniki da kasashen Sin da Amurka suka kulla.

Duk wadannan matakai sun shaida yadda kasar Sin take kokarin zurfafa gyare-gyare a gida, gami da bude kofarta ga sauran kasashe. Sai dai a nasu bangare, wasu 'yan siyasa na kasashen yammacin duniya suna kokarin siyasantar da batun annobar COVID-19, don neman katse huldar ciniki da kasar Sin.

Amma a hakika, dunkulewar duniya waje guda, musamman ma fannin tattalin arziki, wani yanayi ne da ba za a iya canzawa ba, saboda yawancin mutanen duniya suna more wannan tsari, wanda ya ba su damar samun kayayyakin da suke bukata cikin sauki, da farashi mai rahusa. Saboda haka ko da yake annobar COVID-19 tana tasiri kan tsarin tattalin arzikin duniya, hakan na tare da wani wa'adi. Ba za a iya rika daukar ra'ayi na kashin kai ba. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China