Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin tana kokarin kare moriyar bai daya ta daukacin bil Adama
2020-05-25 11:04:24        cri

Mamban majalissar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, mista Wang Yi, ya amsa tambayoyin da 'yan jaridu na kasar Sin da na kasashen waje suka yi masa, a gun wani taron manema labaru da ya gudana jiya Lahadi, a gefen taro karo na 3 na majalissar wakilan jama'ar kasar Sin ta 13, dake gudana a birnin Beijing na kasar Sin. Inda ministan kasar Sin ya yi amfani da alkaluma da misalan wasu hakikanan abubuwa don shaida niyyar kasar Sin ta karfafa hadin gwiwa da sauran kasashe don tinkarar cutar COVID-19, da kare ikon mulkin kai, gami da tunaninta game da makomar duniya. Ta bayanan da ministan ya gabatar, za a iya fahimtar manufar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar ta al'ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya.

Tun bayan barkewar annobar COVID-19 a duniya, wasu 'yan siyasa na kasar Amurka da na sauran kasashen yammacin duniya suna ta kokarin siyasantar da batun, da yunkurin dora wa kasar Sin laifi, da neman lalata huldar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka, wadda ke da muhimmiyar ma'ana ga dorewar zama lafiya a duniya. Dangane da batun, mista Wang Yi ya ce, dole ne bangarorin Sin da Amurka su nemi wata hanya mai dacewa, inda kasashe masu bambancin tsarin siyasa da al'adu za su iya kasancewa tare, gami da kokarin amfanawa juna.

Lalacewar yanayin cutar COVID-19 a kasar Amurka, ta sa wasu 'yan siyasan kasar ke neman karkata hankalin jama'ar kasar, don haka suna ta kokarin ta da cece-kuce kan batutuwan yankin Taiwan, da na Hong Kong na kasar Sin. Game da wadannan aikace-aikace nasu, ministan harkokin wajen kasar Sin ya yi wa wadannan kasashe gargadi, inda ya bukace su don su magance keta layin da kasar Sin ta shata, wato tabbatar da dinkuwar kasar wajen guda. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China