Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ko ina ba za a rasa dokokin tsaron kasa ba
2020-05-25 13:27:40        cri
Yayin da ake tattauna batun kafa dokar tsaron kasa a yankin Hong Kong na kasar Sin a tarukan majalissun kasar, tsohon gwamnan Hong Kong wanda ya wakilci mulkin mallaka da kasar Birtaniya ta yi a Hong Kong, mista Christopher Francis Patten, da wasu 'yan siyasar kasashen yammacin duniya, suna ta korafe-korafen cewa, wai yadda ake neman kafa dokar tsaron kasa ta Sin ya sabawa ra'ayin jama'ar Hong Kong, da hadaddiyar sanarwar da kasashen Sin da Birtaniya suka gabatar a baya, dangane da batun Hong Kong.

Amma a hakika, duk wata kasa dake da cikakken ikon mulkin kai, to, ba za ta rasa dokokin tsaron kasa ba. A kasar Amurka ma, akwai dokoki masu alaka da batun tsaron kasa a kalla 20, inda ake iya yanke wa masu cin amanar kasa hukuncin kisa. Sa'an nan a kasar Birtaniya, dokoki masu alaka da tsaron kasa sun shafi dukkan wuraren kasar, ciki har da yankin dake cin gashin kai na Scotland.

A kan kafa wata kasa mai dimokuradiya, da 'yancin jama'a bisa tushen samun cikakken mulkin kai, da 'yancin kai na wannan kasa. Sai dai wasu 'yan siyasa na kasar Birtaniya wata kila ba su san haka ba. Duk da haka, Sinawa za su gaya musu niyyarsu ta kare wuraren kasa daga mulkin mallaka da na danniya. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China