Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram da 'yan bindiga 599
2020-05-29 12:51:12        cri
Rundunar sojojin Najeriya ta ce, baki daya an kashe mayakan kungiyar Boko Haram da 'yan bindiga kimanin 599 a fadin arewacin Najeriya a lokacin da jami'an tsaron kasar suka jagoranci yaki da 'yan ta'addan cikin wannan wata.

Wata sanarwar da rundunar ta fitar wanda aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Abuja ta ce, jamai'an tsaron sun kaddamar da shirin yaki da bata garin ne tsakanin ranar 6 zuwa 28 ga watan Mayu a arewa maso gabashin kasar, yankin da kungiyar Boko Haram ta shafe sama da shekaru 10 tana kaddamar da ayyukan ta'addanci, da kuma yankunan shiyyar arewa maso yammaci da tsakiyar Najeriya inda 'yan bindiga ke ci gaba da aikata muggan laifuka iri daban daban.

Rundunar sojojin ta ce sakamakon ayyukan sintiri na hadin gwiwa wanda rundunonin sojojin kasar suka kaddamar, an samu matukar raguwar ayyukan ta'addanci da na bata gari a kasar.

A cewar sanarwar sojojin, baki daya mayakan kungiyar Boko Haram 188 aka kashe a lokacin sintirin, wanda ya hada har da manyan kwamandojin kungiyar. Ta kara da cewa, kayayyakin aikin 'yan ta'addan, da manyan bindigoginsu, da maboyarsu duk an tarwatsa su, kana an gano tarin makamai masu yawa a cikin wannan wa'adi. (AHMAD)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China