Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
GDPn Najeriya na watanni ukun farkon shekara ya tsaya a kaso 1.87 bisa dari
2020-05-26 11:32:09        cri
Ma'aunin tattalin arziki na GDP da Najeriya ta cimma a watanni 3 na farkon shekarar bana, ya tsaya kan kaso 1.87 bisa dari tsakanin shekara guda.

Hukumar kididdiga ta kasar ce ta sanar da hakan a jiya Litinin, tana mai cewa, yanayin tattalin arzikin kasar a watannin 3, ya samu koma baya na kaso 0.23 bisa dari, idan an kwatanta da na watanni ukun farkon shekarar 2019, da kuma koma bayan kaso 0.68 bisa dari da kasar ta samu a watanni 3 na karshen shekarar ta bara.

Yanayin da kasar ta gamu da shi ta fuskar tattalin arziki, na da nasaba da halin matsi da tattalin arzikin duniya ya fada, sakamakon kalubalen lafiya da cutar COVID-19 ta haifar, da kuma faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya, baya ga takaituwar hada hadar cinikayyar kasa da kasa. Da kuma koma baya da aka samu a fannonin tattalin arziki da ba na mai ba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China