Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zazzabin Lassa ya hallaka mutane 41 a jihar Bauchi ta Najeriya
2020-05-17 15:14:04        cri
Hukumomi a Najeriya sun ce kimanin mutane 41 da zazzabin Lassa ya kashe a jahar Bauchi dake shiyyar arewa maso gabashin kasar tun bayan bullar cutar a farkon wannan shekara.

Rilwanu Mohammed, shugaban hukumar lafiya matakin farko ta jihar Bauchi, ya fadawa manema labarai cewa, mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 sun yi nasarar warkewa daga cutar sama da wadanda suka kamu da cutar zazzabin Lassa a jahar.

Ya ce, gwamnati ta horas da jami'ai yadda za su gudanar da aikin feshin sinadarin kashe kwayoyin cuta dokin dakile bazuwar cutar a jahar. Ana iya yada cutar zazzabin Lassa ta hanyar yawu, fitsari, ko kashin dake fita daga jikin beraye zuwa ga bil adama da ya yi ta'ammali da su. Galibi, cutar tana da alamu irin na zazzabin maleriya. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China