Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta raba tallafin kayan abinci ga 'yan gudun hijira 38,000
2020-05-15 10:03:17        cri
Gwamnatin Najeriya ta raba kayan abinci ga mutane 38,000 da rikici ya tilastawa ficewa daga muhallansu a wasu sansanoni masu yawa a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Umar Sabi, shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA), reshen jihar Borno, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kayayyakin abincin da aka raba sun hada da garin masara, wake, shinkafa da sauransu wanda aka rabawa mutanen dake rayuwa a sansanin Muna Garage dake Maiduguri.

Wannan mataki na daga cikin kokarin da ake yi na samar da muhimman kayayyakin bukatu ga mutanen dake rayuwa a sansanonin (IDPs) na mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa.

A cewar jami'in, a duk wata hukumar tana samar da tallafin kayan abinci ga mutanen da rikici ya raba su da muhallansu sama da 234, 000 wadanda ke rayuwa a sansanoni, da al'ummonin dake karbar bakuncin mutanen, da wasu yankunan da aka kubutar da su a jihar Borno.

Hare-haren da bangarorin kungiyar Boko Haram suka kaddamar kan fararen hula ya yi sanadiyyar raba mutane masu yawa da muhallansu a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China