Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya: Zaman lafiya ne jigon duk wani ci gaba da Afirka za ta samu
2020-05-26 09:27:59        cri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana zaman lafiya, tsaro, hadin kai da daidaito, a matsayin jigon duk wani ci gaba da nahiyar Afirka ka iya samu. Ya ce nahiyar Afirka ta baiwa duniya sabon buri, duba da yadda ta zabi taken bikin ranar ta na bana, wato "Hana jin karar bindiga yayin da ake yaki da COVID-19".

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a jiya Litinin, cikin sakon sa ga shugabannin Afirka, albarkacin bikin "ranar Afirka" na shekarar 2020, bikin da kungiyar tarayyar Afirka ta AU da hukumar lafiya ta duniya WHO suka kaddamar.

Shugaban na Najeriya ya kara da cewa, idan har shugabannin Afirka na son ganin an cimma nasarar dakatar da jin amon bindigogi a nahiyar, to kamata ya yi su ba da karfi wajen fadakar da al'ummun su, game da muhimmancin alakar dake tsakanin zaman lafiya da kuma ci gaba.

Daga nan sai shugaban na Najeriya ya yi kira ga al'ummun Afirka, da su kirkiro dabarun dakatar da karar bindiga, domin cimma burin wanzar da zaman lafiya, da kuma bunkasa tattalin arzikin nahiyar Afirka.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China