Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNICEF za ta taimakawa yaran Afrika koyon karatu ta intanet a yanayin COVID-19
2020-05-21 10:30:35        cri

Asusun tallafawa kananan yara na MDD (UNICEF) ya sanar cewa, zai yi hadin gwiwa da kamfanin sadarwa na Airtel Africa domin samar da hanyoyin koyon karatu ta intanet da yin musayar kudade ga kanana yara da iyalansu a yankin da ke kudancin hamadar Saharar Afrika.

Karkashin hadin gwiwar, UNICEF da kamfanin Airtel Africa za su yi amfani da fasahar zamani ta wayar hannu domin amfanawa yara 'yan makaranta kimanin miliyan 133 wadanda rufe makarantu ya shafa a kasashe 13 na yankin da ke kudancin hamadar saharar Afrika a lokacin da ake fama da annobar COVID-19.

Cikin wata sanarwa da UNICEF ta fitar a Nairobi ta ce, shirin zai taimakawa iyalai wajen samun karin kudaden da za su gudanar da rayuwarsu a yayin da ake cikin halin barazanar kiwon lafiya da matsalar tabarbarewar tattalin arziki sakamakon annobar COVID-19.

A cewar UNICEF, masana sun yi gargadin illar da rufe makarantun zai iya shafar yanayin karatun kananan yara musamman wajen samun koma baya ga fannin karatunsu.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China