Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan makamashin Zimbabwe: Sin na inganta hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da cutar COVID-19
2020-05-20 19:39:30        cri
Yayin babban taron kiwon lafiyar kasa da kasa karo na 73 da aka gudanar ta kafar bidiyo, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da shawarar cewa, ya kamata a kara tallafawa kasashen Afirka, a yunkurinsu na dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19. Haka kuma, ya yi alkawarin cewa, kasar Sin za ta fito da wani tsarin hadin kan asibitoci 30 na Sin da Afirka, da gaggauta gina hedkwatar cibiyar shawo kan cututtuka ta Afirka, domin kara karfin Afirka na yaki da cututtuka.

Game da hakan, ministan makamashi da wutar lantarki na kasar Zimbabwe Forune Chasi ya yabawa kasar Sin, dangane da taimako da goyon baya da take baiwa kasashen Afirka, domin kara karfinsu na yaki da cutar. Ya ce, lamarin ya nuna karfin kasar Sin, a matsayinta na babbar kasa a duniya, dake sauke alhakin dake wuyanta yadda ya kamata.

Ya ce, taimakon da kasar Sin ta kara samar wa kasashen Afirka, ya sa kaimi gare ni. Yanzu ina ganin cewa, tabbas Zimbabwe za ta cimma nasarar dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China