Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta amince da shawarar kafa dokar tsaron kasa a yankin Hong Kong
2020-05-28 19:56:35        cri

Mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Wang Chen, ya bayyana a makon jiya cewa, kasarsa tana shirin amincewa da dokokin tsaron yankin musamman na Hong Kong, bayan da zaman majalisar ya kada kuri'ar amincewa da wannan kudiri.

Yayin zaman rufe taro na uku na wakilan NPC karo na 13 a yau, wakilan baki daya sun amince da shawarar da majalisar ta gabatar na kafa da inganta tsarin doka da hukunci a yankin musamman na Hong Kong da tabbatar da tsaron kasa.

Wang Chen ya ce, tsarin doka da yadda ake yanke hukunci wajen tabbatar da tsaron kasa suna da rauni a yankin na Hong Kong. Kana idan aka yi la'akari da halin da ake ciki a yankin, wajibi ne a kara zage damtse wajen kafawa da inganta tsarin doka da yanke hukunci don tabbatar da tsaro a yankin na Hong Kong.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China