Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin tana fatan samun kyakkyawan ci gaban tattalin arziki a wannan shekara
2020-05-28 19:29:44        cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya bayyana cewa, muddin aka yi nasara a muhimman fannoni guda shida da aka zayyana, babu shakka kasarsa tana fatan samun kyakkyawan bunkasar tattalin arziki a shekarar 2020 da muke ciki.

Li wanda ya bayyana haka yayin taron manema labarai bayan kammala zaman shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Alhamis din nan, ya ce, muhimman fannoni shidan da ya ke batu sun hada da samar da ayyukan yi, da muhimman bukatun rayuwa, da sakarma kasuwa mara, da tsaron abinci, da dorewar ayyukan masana'antu da samar da kayayyaki, sai kuma tafiyar da ayyukan gwamnatoci a matakai na kasa. Kana a kara zaga damtse wajen tabbatar da tsaro a fannoni uku na farko.

Firaminista Li, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta dauki managartan matakai, maimakon matakai na rage radadi don bunkasa tattalin arziki.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China