Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zaman majalisar NPC ya amince da kundin dokar zamantakewar al'umma
2020-05-28 19:34:08        cri

A yau ne, zaman taro na uku na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13, ya kada kuri'ar amincewa da kundin dokar zamantakewar al'umma da aka dade ana tsammani.

Baya ga manyan tanade-tanade da kanana kudurori, kundin zamantakewar al'umma, shi ne kundin dokar zaman takewar al'umma irin sa na farko a sabon zamani da ake ciki a duniya, yana kuma da sassa shida da suka shafi hakkin bil-Adama, da 'yancin rayuwa, da batun da ya shafi aure da iyali da gado da biyan diya kan barnar da aka haddasa.

Wakilan sun bayyana cewa, gyara fasalin dokar, ba ya nufin kafa sabuwar doka game da zamantakewar al'umma, maimakon haka wani tsari na sanya dokoki da ka'idojin da ake amfani da su a baya, da yi musu gyaran fuska da kuma inganta su, ta yadda za su dace da sabbin yanayin da ake ciki a wuraren da za a aiwatar da su.

A ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2021, ake sa ran dokar za ta fara aiki.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China