Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babu wanda zai amfana idan an lalata dangantakar Sin da Amurka
2020-05-28 19:34:08        cri
Firaminista Li Keqiang na kasar Sin ya bayyana a yau Alhamis cewa, idan an lalata dangantakar Sin da Amurka, babu wani bangaren zai ci moriya, kuma duniya ma za ta ji radadi. Don haka, kamata ya yi bangarorin biyu su kokarta wajen raya dangantakarsu bisa tushen mu'amala da hadin-gwiwa gami da matsayar da aka cimma tsakanin shugabannin kasashen biyu.

Li ya jaddada a wajen taron manema labarai cewa, ya kamata hadin-gwiwar Sin da Amurka a fannin kasuwanci ta mutunta ka'idojin kasuwanni, kana manyan masu kamfanoni za su iya yanke shawara, ita kuma gwamnati za ta iya kafa dandali tsakaninsu. Li ya ce, duba da irin bambance-bambancen dake tsakanin kasashen biyu, a fannonin tsarin kasa da al'adu da kuma tarihi, dole ne a samu sabani tsakaninsu, amma abu mafi muhimmanci shi ne yadda za'a tinkare su ta hanyar da ta dace. Akwai bukatar bangarorin biyu su fadada moriyarsu ta bai daya, da daidaita sabaninsu, da girmama babbar moriyarsu gami da abubuwan da suke jawo hankalinsu dukka, domin amfana tare.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China