Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Sin: Sin na fatan karfafa hadin-gwiwa da kasa da kasa don yakar COVID-19
2020-05-28 19:07:05        cri
Firaminista Li Keqiang na kasar Sin ya bayyana a yau Alhamis cewa, kasarsa na sa ran fadada hadin-gwiwa da sauran kasashen duniya, domin samun nasara a kan cutar numfashi ta COVID-19.

Game da batun asalin kwayar cutar, Li ya ce, a yanzu haka kasa da kasa sun himmatu wajen nazarin allurar rigakafin cutar, da magunguna gami da sinadarin gwajin kwayar cutar, wadanda dukkansu mallakin daukacin al'ummar duniya ne. Kasar Sin na fatan fadada hadin-gwiwa da kasa da kasa a wani kokari na samun galaba ta karshe kan wannan cutar dake addabar fadin duniya baki daya.

Firaminista Li ya kuma jaddada cewa, a halin yanzu duniya na fuskantar manyan kalubaloli a fannonin da suka shafi dakile yaduwar annobar da kuma farfado da tattalin arziki da zamantakewar al'umma, al'amarin dake bukatar hadin-gwiwa tsakanin kasa da kasa.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China