Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
SADC ta bukaci mambobinta su cire shinge don bunkasa tattalin arziki
2020-05-28 10:55:35        cri

Manyan jami'an kungiyar raya shiyyar kudancin Afrika SADC sun bukaci mambobin kasashen shiyyar da su cire dukkan shingayen kasuwanci da nufin bunkasa tattalin arzikin shiyyar.

Wilbert Ibuge, babban sakataren ma'aikatar harkokin waje da hulda da gabashin Afrika na kasar Tanzania, ya ce, rokon da aka yi na neman a cire shingen kasuwanci a tsakanin mambobin kasashen kungiyar SADC ya biyo bayan taron manyan sakatarorin kungiyar SADC da aka gudanar ne na tsawon kwanaki uku ta kafar bidiyo.

Ibuge, wanda ya jagoranci taron, ya sanarwa 'yan jaridu a birnin kasuwancin kasar Dar es Salaam cewa, jami'an mambobin kungiyar SADC sun bukaci a bude kan iyakokin kasashen wadanda ke da yawan jama'a miliyan 345 domin saukaka harkokin kasuwanci a tsakaninsu. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China