Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin SADC sun cimma matsayar magance barazanar tsaro dake damun shiyyar
2019-08-19 11:23:33        cri

A yayin taron da shugabannin kungiyar raya yankin kudancin Afrika (SADC) suka gudanar a kasar Tanzania sun amince za su dauki matakan magance barazanar tsaro dake ci gaba da fuskanta a shiyyar, wadanda suka hada da ta'addanci, a cewar sanarwar bayan taron da kungiyar ta fitar a jiya Lahadi.

An fitar da sanarwar ne a karshen taron kolin shugabannin kasashen kungiyar SADC karo na 39, wanda aka gudanar a birnin Dar es Salaam, hedkwatar kasuwancin kasar ta Tanzaniya, shugabannin sun cimma matsaya daya wajen daukar kwararan matakan dakile barazanar tsaro dake addabar shiyyar, musamman matsalar ayyukan ta'addanci da laifukan kan iyakokin kasashen.

A cewar sanarwar bayan taron, shugabannin kasashe mambobin kungiyar ta SADC 16, sun bukaci a ba da fifiko wajen aiwatar da yarjejeniyar SADC game da tsara dabarun yakar ayyukan ta'addanci a shiyyar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China