Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
SADC ta bukaci taimakon kasa da kasa wajen yaki da farin dango
2020-02-23 16:43:54        cri
Ministocin ma'aikatun yaki da bala'u na kungiyar raya kasashen shiyyar kudancin Afrika (SADC), sun bukaci taimakon kasa da kasa da su taimakawa shiyyar wajen yaki da annobar farin dango dake ci gaba da bazuwa a shiyyar.

A takardar bayan taron da kungiyar ta fitar a daren Juma'a a karshen taron wuni guda da aka gudanar a tsibirin Zanzibar, ministocin sun ce yadda farin dangon ke ci gaba da yin kaura zuwa yankunan zai haifar da mummunar illa na karancin abinci ga shiyyar wanda take da yawan al'umma kimanin miliyan 345.

Ministocin sun nuna damuwa matuka na neman daukin gaggawa wajen dakile kwari da nau'ikan jajayen fari da farin hamada wadanda ke haifar da tabarbarewar al'amurra na karancin abinci a shiyyar.

Sun bukaci mambobin kasashe 16 na SADC da su hada kai don yin aiki tare da yin musayar bayanai da nufin dakile annobar farin dangon dake ci gaba da yin hijira zuwa shiyyar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China