Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Namibia ta mika ragamar majalissar kasuwanci ta SADC ga Tanzania
2019-08-06 14:05:39        cri
Kasar Namibia, wadda ke jagorancin majalissar kasuwanci, ta kungiyar raya kasashen kudancin Afirka ta SADC, ta mika ragamar majalissar ga Tanzania. A jiya Litinin ne Charity Mwiya na Namibia, ya mika ragamar majalissar ga Salum Shamte na Tanzania.

Mr. Mwiya ya godewa kungiyar SADC mai kasashe mambobi 16, bisa amincewar ta ga muhimmancin sassa masu zaman kan su, a matsayi bangare mai tasiri ga ci gaban hada hadar zuba jari, da samar da ci gaba.

A nasa tsokaci, sabon jagoran majalissar, kuma shugaban asusun sassa masu zaman kan su a Tanzania ko TPSF a takaice Salum Shamte, cewa ya yi, abu ne da ya wajaba, sassan gwamnati da na masu zaman kan su, su yi hadin gwiwa don magance kalubalen dake haifar da koma baya ga nahiyar Afirka.

A shekarar 1992 ne aka kafa kungiyar SADC, kungiyar da ta mayar da hankali ga hade sassan kudancin Afirka wuri guda, da yaki da talauci, ta hanyoyin bunkasa tattalin arziki, da wanzar da zaman lafiya da tsaro. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China