Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyar SADC za ta hada shirye-shiryenta da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya
2019-08-05 10:10:12        cri

Kungiyar raya yankin kudancin Afrika SADC, za ta hada shirye-shiryenta da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya ta kasar Sin, domin aiwatar da dabarunta na bunkasa ayyukan masana'antu da zamanintar da tattalin arziki.

Johansein Rutaihwa, babban jami'in shirye-shirye kan ayyukan masana'antu da takara a sakatariyar SADC, ya ce kungiyar za ta hada shirye-shiryenta da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, wajen aiwatar da manufofin bunkasa masana'antu, musammam kan ginin ababen more rayuwa.

Jami'in ya shaidawa wani taron manema labarai a birnin Dar es Salaam na Tanzania gabanin makon bunkasa masana'antu da baje koli na kungiyar SADC wanda za a fara yau Litinin cewa, shawarar Ziri Daya da Hanya Daya ta kasar Sin, ita ce mafi dacewa a hada ta da shirye-shiryen kungiyar kan bunkasa ayyukan masana'antu.

Ya ce dabarun bunkasa masana'antu na kungiyar zai mayar da hankali kan sarrafa amfanin gona da sarrafa ma'adinai da hada magunguna.

Taken makon bunkasa masana'antun da baje koli na SADC karo na 4 shi ne: kyakkyawan yanayi domin dorewar ci gaban masana'antu da kara cinikayya tsakanin kasashen kungiyar da samar da aikin yi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China