Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jam'iyyun siyasar Afrika: Hadin gwiwar Sin da Afrika ta fuskar yaki da COVID-19 na kara yaukaka dangantakarsu
2020-04-30 10:21:36        cri
Jam'iyyun siyasa da fitattun mutane daga kasashen Afrika, sun yabawa matakin kasar Sin na taimakawa kasashensu a yaki da annobar COVID-19, wanda ya karfafa yakininsu na cin nasara kan cutar.

A sakon da suka aika wa JKS a baya bayan nan, jam'iyyun sun bayyana cewa, al'ummun Sin da Afrika na da fahimtar juna, kuma abotarsu ta kara karfi bayan sun hada hannu wajen yaki da cutar COVID-19.

Sun kara da cewa, a shirye kasashen Afrika suke su hada hannu da kasar Sin wajen samar da al'umma mai cikakkiyar lafiya ga bil adama.

John Boadu, sakatare janar na jam'iyyar NPP ta kasar Ghana, ya ce Ghana na ba dangantakarta da kasar Sin muhimmanci sosai, kuma tana yabawa irin taimakon da Sin ke bayarwa ga ci gaban kasar.

Shi kuwa kwamishina mai kula da kawancen Sin da Jam'iyyar Alliance for the Republic Party ta Senegal, kuma mashawarcin shugaban kasar, Thierno Doura Balde, ya ce kasarsa na godiya ga Sin bisa kula da jami'anta dake Sin, duk da yanayin da take ciki.

Ya ce kawancen Sin da Afrika dadaddiya ce, kuma yana fatan Sin za ta ci gaba da goyon bayan nahiyar Afrika wajen yaki da COVID-19 da zurfafa hadin gwiwarsu a fannin kiwon lafiya da kuma gina al'umma mai lafiya a Sin da Afrika. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China