Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jawabin Xi Jinping a yayin taruka biyu ya kara nuna muhimmancin jama'arsa
2020-05-27 20:35:39        cri
A lokacin taruka biyu na kasar Sin wato taron majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa (CPPCC) da na majalisar wakilan jama'ar kasar (NPC) na bana, a yayin da yake ganawa da 'yan majalisun biyu, shugaban kasar Xi Jinping ya sha ambato muhimmancin jama'a, wanda kuma ya kasance jimlar da ke jawo hankulan mutane sosai a yayin tarukan biyu.

Shekarar bana shekara ce ta musamman. A farkon wannan shekarar ce, kasar Sin ta gamu da babban al'amarin lafiyar jama'a mai saurin yaduwa, har ma ta shafi yawancin yankunan kasar, kuma mai wahalar kandagarki da shawo kanta tun bayan aka kafa sabuwar jamhuriyar jama'ar kasar. Bayan kokarin da daukacin al'ummar kasar suka yi, a cikin kimanin watanni 3 kawai kasar ta yi nasarar dakile annobar ta COVID-19. Ko shakka babu, dakile cutar da kokarin farfado da ci gaban tattalin arziki sun kasance batutuwan da suka fi jawo hankali a yayin tarukan biyu.

A watan Maris, wato lokacin da birnin Wuhan na lardin Hubei na kasar ya fi shan wahala wajen kandagarkin cutar, shugaba Xi Jinping ya tafi Wuhan don yin bincike da nazari da kuma ba da jagoranci, inda ya jaddada cewa, dole ne a yi kokarin tabbatar da zaman rayuwar mazauna wurin yadda ya kamata.

A yammacin ranar 24 ga wata, a yayin taron tattaunawa da tawagar wakilan lardin Hubei, wata wakiliar majalisar wakilan jama'a ta yi sujjada ga shugaba Xi Jinping, ta ce, a madadin mazauna unguwarsu ne tana nuna godiya ga shugaba Xi.

A yayin tattaunawar, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, wani muhimmin aikin gaggawa dake gaban lardin Hubei, shi ne yin namijin kokari kan ayyukan dakile annobar da samu ci gaban tattalin arziki da zaman takewar al'umma.

Baya ga haka, shugaba Xi Jinping ya bukaci a aiwatar da manufofi da matakan da kwamitin tsakiya ya amince don nuna goyon baya ga Hubei ba tare da bata lokaci ba. Kana ya gabatar da cewa, ya kamata a mayar da hankali kan wasu matsalolin da ka iya kunno kai bayan annobar.

"Ana kokarin inganta bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma ne domin biyan bukatun jama'a don inganta rayuwarsu", "Ya kamata a tabbatar da ganin an aiwatar da matakai daya bayan daya a ko wace shekara, ta yadda jama'a za su fahimci canje-canje da samun hakikanin moriya"……Wadannan umarni da gargadi da Xi Jinping ya bayar a lokacin tarukan biyu na bana, sun nuna manufar ci gaba da kasar Sin ke bi wato muhimmancin jama'a. Sun kuma taimakawa kasashen duniya su kara fahimtar dalilan da suka sanya kasar Sin ta samu babbar nasara wajen dakile annobar cikin gajeren lokaci, da yadda ta iya tabbatar da cimma burinta a fannonin bunkasuwar tattalin arziki da zaman takewar al'umma. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China