Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Kyautatuwar tattalin arzikin Sin za ta taimakawa kyautata tattalin arzikin duniya
2020-02-24 21:05:05        cri

A jiya Lahadi, an yi wani taro mai girma ta telabijin da wayar tarho a kasar Sin, inda kimanin mutane dubu 170 suka halarci taron. A wajen taron mai taken "Daidaita ayyukan hana yaduwar cutar COVID-19 da raya tattalin arziki", shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, "Matukar an fitar da cikakken karfin Sin na raya sana'o'i, za a iya cimma burin da aka sanya gaba, na neman ci gaban tattalin arziki, da zaman al'ummar kasar na wannan shekara."

Yanzu haka an samu ci gaba sosai a fannin dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Sin. Saboda haka, karin kamfanonin kasar na kokarin maido da ayyukansu, lamarin da ya taimakawa fitar da karfin kasar ta fuskar raya tattalin arziki.

Kasancewar adadin ma'aunin GDP (yawan kudin kayayyakin dake samarwa a gidan wata kasa) na kasar Sin ya kai kimanin kashi 16% na GDPn duk duniya, kasar ta samar da gudunmawar fiye da kashi 30% na karuwar tattalin arzikin duniya.

Ta la'akari da wannan yanayin da ake ciki ne, daukar kwararrun matakai masu karfi a kasar Sin wajen tinkarar annoba, zai sa kasar ta samu karin damammakin kyautata yanayin tattalin arzikinta, gami da kiyaye wani yanayi na zaman karko ga tattalin arzikin duniya. Idan an yi la'akari daga wannan fanni, yadda kasar Sin take kokarin hana yaduwar cutar, gami da maido da ayyuka, ba kawai zai amfani kanta ba ne, har ma zai haifar da alfanu ga daukacin al'ummun duniya.

Hakika matakan sun nuna yadda kasar Sin ke kokarin sauke nauyin ta, don tabbatar da ci gaban tattalin arzikin duniya da moriyar jama'ar kasa da kasa. Ban da haka, ana ganin karin wasu abubuwan dake taimakawa raya tattalin arzikin kasar ta Sin.

Da farko, manyan kasuwannin kasar da al'ummun kasar masu dimbin yawa, su ne ginshikan ci gaban tattalin arzikin kasar. Salmaan Jaffery, babban jami'i ne mai kula da raya kasuwanci a cibiyar hada-hadar kudi ta Dubai na hadaddiyar daular Larabawa UAE, wanda ya taba bayyana cewa, kasar Sin na da dimbin jama'a dake bukatar sayen kayayyaki, gami da managartan manufofi, don haka duk da cewa annobar COVID-19 za ta yi tasiri ga tattalin arzikin kasar cikin wani kankanin lokaci, a hannu guda hakan ba zai hana kasar samun ci gaba ba, idan an yi hasashe game da yanayin da ake ciki a dogon lokaci mai zuwa.

Sa'an nan na biyu, bayan bullar annobar, kasar Sin ta yi amfani da wasu fasahohin zamani, irisu 5G, da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam AI, wajen dakile yaduwarta. Dangane da hakan, wata masaniya dake aiki a sashen nazarin manufofin tattalin arziki na kasar Sin a kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki da ci gabansa OECD, Margit Molnar, ta ce yayin da annoba ke yin matsin lamba ga sana'o'in gargajiya na kasar Sin, tana kuma samar da damammaki ga ci gaban sana'o'i masu alaka da sabbin fasahohin zamani na sadarwa, da injuna masu kwakwalwa.

Ban da wannan kuma, yayin da ake kokarin dakile yaduwar cutar COVID-19, ana iya ganin wasu bangarori da su gurgunta, musamman ma abubuwan da suka shafi kayayyakin kare lafiyar jama'a, da ayyukan tinkarar lamarin ta-baci, da tsarin adana kayayyaki, da dai makamantansu. Duk da haka, wadannan fannoni da ba su yi inganci sosai ba tukuna, wato dai bangarori ne da za a zuba jari a cikinsu, don neman ganin ci gaban su a nan gaba.

A nasa bangare, kamfanin Reuters ya gudanar da wani bincike a kwanan baya, inda ya gayyaci wasu masanan ilimin tattalin arziki 40 daga yankunan Asiya, da Turai, da kuma Amurka, don su yi hasashen makomar tattalin arzikin kasar Sin. Inda dukkan masanan 40 suka kyautata zaton cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai farfado, gami da samun karuwa sosai a rubu'i na biyu, wato tsakanin watan Afrilu da na Yunin bana. (Mai Fassarawa: Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China