Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Yadda 'yan siyasar Amurka suke son kudi ya nuna halayyarsu na zalunci
2020-03-21 21:19:11        cri

A kwanakin nan, kafofin watsa labaru na kasar Amurka da jama'ar kasar dukkansu suna fushi matuka saboda wani abu.

A ranar 13 ga watan Fabrairu, shugaban kwamitin aikin leken asiri na majalisar dattawan kasar Amurka, Richard Burr, ya sayar da hannayen jarin da shi da matarsa suka mallaka, wadanda darajarsu ta kai tsakanin dalar Amurka dubu 628 zuwa miliyan 1.72.

Kasancewarsa daya daga cikin mambobin kwamitin aikin lafiya na majalisar dattawan kasar Amurka, Richard Burr ya taba halartar aikin tsara shirin dokar tinkarar cututtuka masu yaduwa a kasar. A cewar gidan rediyon NPR na kasar Amurka, bayan bullar cutar COVID-19 a kasar, Mista Burr ya kan saurari rahotannin majalisar dattawa dangane da yanayin cutar a kai a kai. Amma bai taba nuna ma jama'ar kasar hadarin cutar ba, maimakon haka kullum yana cewa "babu wata matsala" ga aikin dakile yaduwar cutar COVID-19 a kasar Amurka. Har ma a ranar 7 ga watan Fabrairu, Richard Burr ya taba bayyanawa a shafin intanet na kamfanin watsa labarai na Fox cewa, aikin dakile cutar a kasar Amurka yana da inganci sosai, inda ya ce "ya fi na lokacin baya inganci". Sai dai bayan mako guda, ya fara sayar da dimbin hannayen jarinsa. Lamarin da ya sa ake tuhumar cewa, ya san hadarin annobar, amma ba ya son fadi.

Ban da wannan kuma, an ce wasu 'yan majalisar dattawa 3 su ma sun sayar da hannayen jari da yawa, kusan lokaci daya da mista Burr ya sayar da nasa hannayen jari. Kuma wadannan 'yan majalisar dattawa 3 su ma sun taba sauraron rahoton da aka gabatar dangane da cutar a majalisarsu.

Wadannan batutuwa sun sa jama'ar kasashe daban daban sanin cewa: Kudi shi ne abu mafi muhimmanci, har ma ya fi rayukan mutane, a idanun wasu 'yan siyasar kasar Amurka.

Bisa bayanan da kafofin watsa labarun kasar Amurka suka gabatar, hukumar leken asiri ta kasar Amurka ta taba yin gargadi cikin sirri har sau da dama a watannin Janairu da Fabrairun bana, cewa kwayoyin cutar COVID-19 ka iya haddasa babbar matsala da ta shafi duk duniya baki daya. Duk da haka wasu 'yan siyasar kasar Amurka sun yi kokarin boye bayanan, ko kuma neman kawar da tasirinsu, maimakon daukar matakai masu dacewa. Daya daga cikin dalilan da suka sa mutanen yin haka, a cewar wasu manazarta harkokin yau da kullum, shi ne tsoron haifar da mummunan tasiri ga tattalin arzikin kasar. Saboda "ci gaban fannin tattalin arziki" shi ne abu mafi muhimmanci a idon gwamnatin kasar Amurka na yanzu, kana shugaba Donald Trump na dogaro kan wannan batu ne yayin da yake kokarin neman sabunta wa'adin mulkinsa. Don haka, wani abu mai ban mamaki ya abku, wato: ko da yake gwamnatin kasar Amurka ta yi tafiyar hawainiya a fannin aikin dakile yaduwar cutar COVID-19, amma ta dauki matakan ceto kasuwar hannayen jari cikin saurin gaske, sai dai bai amfani ba. Zuwa ranar 20 ga watan da muke ciki, darajar hannayen jari a kasuwar Amurka ta sauka zuwa wani matsayin da aka samu kafin shugaba Donald Trump ya hau karagar mulki.

Ban da wannan kuma, batun gwaje-gwajen kwayoyin cuta shi ma ya nuna manufar kasar Amurka ta dora muhimmanci kan kudi. Ta yaya za a samu a yi gwaje-gwajen kwayoyin cutar COVID-19 a kasar Amurka? Jaridar New York Time ta ba da amsa cewa, sai mutum ya zama mai kudi tukuna.

Wajen wani taron menama labaru da ya gudana a fadar White House ta kasar Amurka a ranar 18 ga watan da muke ciki, wani dan jarida ya tambayi shugaba Donald Trump cewa, "Ko za a sanya wani mai alaka da manyan kusoshi, cikin jerin masu jiran samun gwaje-gwaje?", shugaba Trump ya amsa cewa, "A'a", amma ya kara da cewa, "watakila zaman rayuwar mutum kamar haka yake, wani lokaci ma irin wannan batu na abkuwa."

To, sai dai yayin da ake fama da wata annoba mai kisa, "zaman rayuwa haka yake" magana ce da ya dace wani shugaban kasa ya fada? (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China