Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Wadanda ke wasa da wuta, su wuta ke kisa
2020-02-24 22:30:02        cri

A farkon wannan wata da muke ciki, Jaridar "The Wall Street Jounal (WSJ)" ta kasar Amurka ta wallafa wani sharhi mai taken "Kasar Sin ta kasance mai fama da cututtuka a Asiya", wanda ya nuna ra'ayi na bambancin kabila, kuma ya wulakanta kasar Sin. Wannan lamari ya harzuka jama'ar kasar Sin, gami da fusatar da al'ummun kasashe daban daban.

Da ma jaridar WSJ mai neman ta da rikici ce, yanzu dangane da wannan al'amarin, ma iya cewa "Duk wadanda ke wasa da wuta, su wuta ke kisa."

An ce a ranar 20 ga watan da muke ciki ne, wasu ma'aikatan jaridar WSJ 53 dake aiki a kasar Sin, suka yi hadin gwiwa wajen aikewa da wani sako ga shugaban kamfanin jaridar, don bukatar a gyara taken labarin da aka sanya mai ma'anar wulakanta kasar Sin, da neman gafara daga wadanda aka keta hakkinsu ta labarin.

Ma'aikatan sun bayyana a cikin wasikar cewa, "Batun bai shafi ikon edita na zaman kansa ba, kuma bai shafi batun raba tsarin labarai da na bayanan sharhi ba. Saboda taken wannan labari kuskure ne, kuma ya fusata al'ummomi daban daban, ciki har da Sinawa."

Amma abin takaici shi ne, ko da yake ma'aikatan sun dau wannan mataki, kuma kasar Sin ta bayyana kin amincewa da yadda aka wallafa sharri sau da dama, sa'an nan 'yan asalin kasar Sin fiye da dubu 100 sun yi zanga-zanga a gaban fadar White House ta kasar Amurka, don neman jaridar WSJ ta nemi gafara. Amma duk da haka, jaridar ta ce ayyukan watsa labarai, da wallafa sharhi mabanbantan harkoki ne masu zaman kansu, don haka ba ta da alhaki game da abun da aka rubuta.

Jaridar tana amfani da wannan dalili ne domin kaucewa nauyin da ya kamata ta dauka. Kuma har yanzu ta ki neman gafara. Ban da haka, lokacin da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar da soke takardun aiki na wasu wakilan jaridar WSJ 3 dake birnin Beijing na kasar Sin a kwanan baya, don kare hakkin kasar bisa doka, sakataren harkokoin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya yi suka kan kasar Sin, yana zargin ta da keta 'yancin magana.

Yanzu haka, wasikar da ma'aikata 53 na jaridar WSJ suka rubuta ta shaida cewa, wannan batu ba wani al'amari ne na keta 'yancin magana ba, maimakon haka wani batu ne na nuna bambancin kabila.

A wannan lokaci mai muhimmancin matuka, da kasar Sin take iyakacin kokarinta wajen dakile yaduwar cutar COVID-19, aikace-aikacen jaridar WSJ sun sanar da wata alama mai hadari: Cewa ana fuskantar dawowar ra'ayin nuna bambancin kabila, musamman ma irin na kin jinin kasar Sin, ko kuma Sinawa a kasar Amurka, da sauran kasashen yammacin duniya. Wannan yanayi zai gurgunta yunkurin hana yaduwar annobar COVID-19, gami da haifar da matsala ga kokarin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a duniyarmu. (Mai Fassarawa: Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China