2020-05-17 19:45:54 cri |
Sannan shugaba Donald Trump na Amurka ya ce, tun daga ran 11 ga watan Janairun bana ne kasarsa ta fara nazarin allurar rigakafin annobar cutar Korona. A ran 12 ga watan Janairu ne kasar Sin ta sanar wa kungiyar kiwon lafiya ta kasa da kasa WHO da bullar sabuwar cutar numfashi ta Korona. Wannan ya shaida cewa, kasar Amurka ta riga kasar Sin sanin bullar annobar a duniyarmu, amma ta boye lamarin, ba ta sanar wa kungiyar WHO ba.
Sanin kowa ne, kasar Amurka kasa ce mafi karfi a fannonin kimiyya da fasaha, da tattalin arziki, da kuma kiwon lafiya a duk fadin duniya. Shugabanin kasar ma su kan ce, kasar Amurka na sahun gaba a duk duniya, tana kokarin kiyaye hakkin bil Adam, ba ta rufe kome ba. Saboda haka, a farkon lokacin bullar annobar, daukacin bil Adam na duk duniya sun yi fatan kasar Amurka ta zama wani abin misali, da taka muhimmiyar rawa da kuma bayar da gudummawarta kamar yadda ake fata wajen dakile annobar COVID-19 a duk fadin duniya. Amma yanzu, ka ga, me ya faru?
A ranar 4 ga watan Maris, gwamnatin kasar Amurka ta sanar da dakatar da sanar da adadin masu harbuwa da cutar, da adadin wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar ga jama'a. Kuma har yanzu ba a san hakikanin yawan sojoji da hafsoshin da suka kamu da cutar ko suka mutu sakamakon cutar a rundunar sojin Amurka ba.
Bugu da kari, a ranar 8 ga watan Agustan bara, ba zato ba tsammani, kasar Amurka ta rufe sansanin nazari da gwajin makamai masu guba da na halittu na Port Detrick ba tare da sanar da dalili ba. Ko da yake an ce, ana nazari da gwajin makamai masu guba da na halittu a wannan sansanin Port Detrick, amma a hakika dai, an adana kusan dukkan samfurorin kwayoyin cutuka mafi hadari na duniya a wannan sansani. Kasar Amurka ta nazarci makamai masu guba ko na halittu da karfinsu zai yi kusan daidai da makaman nukiliya a sansanin. Ko kasar Amurka ta taba sanarwa jama'a da sauran kasashen duniya wannan bayani?
Dadin dadawa, a kwanan baya, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta sanar da cewa, a yankunan dake kewayen kasashen Rasha da Sin, a asirce ne, kasar Amurka ta kafa dakunan nazari da gwajin sinadarai masu guba da halittu 15, kuma gaba daya, ta kafa irin wadannan dakuna wajen dari 2 a duk fadin duniya. Me ake nazari a cikin wadannan dakuna? Ko za su kawo barazana ga mazauna yankunan da suke? Yanzu muna son sanin me take boyewa a cikin wadannan dakunan nazari da gwajin sinadarai masu guba da na halittu? Amma har yanzu kasar Amurka ba ta fadi kome ba, ta yi shiru kawai.
Sabo da haka, ko da yake gwamnatin kasar Amurka ta kan cuci daukacin dukkan kasashen duniya cewa, ba ta boye kome ba, tana tafiyar da kome da kome a fili, amma hakikanin abubuwan da suka faru da wadanda suke faruwa a gabanmu sun shaida cewa, kasar Amurka na yunkurin rufe dukkan abubuwan da take son boyewa, ko da yake mai yiyuwa ne wadannan abubuwa za su kawo barazana ga jama'ar duk duniya.
Jama'a abokan arzikinmu, ko kasar Amurka ta zama abin misali ga kowa wajen tsaron jama'ar duk duniya, ko ta zama sarauniyar boyewa, har ma sarauniyar keta hakkin dan Adam a duk duniya a yanzu? Ina fatan ku ba ni amsa. (Sanusi Chen)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China