Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zumuncin dake tsakanin Sin da Afrika ya samu karfafu sakamakon hadin gwiwarsu wajen yakar annobar COVID-19
2020-05-04 17:30:56        cri

Jaridar People's Daily wadda ake wallafa ta a Beijing, fadar mulkin kasar Sin, a kwanan baya ta wallafa wani rahoto dake nuna cewa, manyan jami'an siyasar Afrika da shugabannin jami'iyyun siyasa na kasa da kasa sun aike da wasiku ga sashen hulda da kasashen waje na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, inda suka yi matukar nuna yabo da jinjina game da matakan da Sin take dauka a zahiri wajen tallafawa kasashen Afrika a yaki da cutar COVID-19. Haka zalika shugabannin sun yabawa aniyar gwamnatin Sin wajen kare lafiya da hakkokin jama'ar kasashen Afrika dake kasar Sin. Sun yi amanna cewa, kyakkyawar dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika za ta dore duk wuya duk rintsi, kuma Sin da Afrika za su gina tsarin hadin gwiwa na kut-da-kut don samar da kyakkyawar makoma ga dukkan alumma ta hanyar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika na yaki da annobar COVID-19.

Lawal Sale, wani masani mai sharhi kan harkokin kasa da kasa a Najeriya, ya wallafa wani rahoto mai taken "Annobar COVID-19: Najeriya da Sin suna kokari tare", wanda aka wallafa a jaridar ta Peoples Daily inda ya yi nuni da cewa, ba zai yiwu a gurgunta hadin gwiwar zumunta dake tsakanin kasashen biyu ba, kana goyon bayan junansu ya nuna irin dadadden zumuncin dake tsakanin bangarorin biyu.

Idan za mu iya tunawa, tun bayan barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Sin, gwamnatin kasar ta himmatu wajen daukar matakan da suka dace cikin gaggawa, misali killace birnin Wuhan inda aka samu barkewar cutar gami da tantance daukacin mutanen da suka yi cudanya da wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar, hakan ya sa ta yi nasarar hana yaduwar annoba. Wadannan matakai da kasar Sin ta dauka sun janyo mata yabo daga shugabannin duniya da na kungiyoyin kasa da kasa musamman hukumar lafiya ta duniya WHO da MDD da dai sauransu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana daga cikin shugabannin kasashen duniya da suka nuna goyon baya da kuma jinjina ga matakan da gwamnatin Sin ta dauka wajen dakile annobar COVID-19 cikin gaggawa. Duk da irin fadi tashin da kasar Sin ke yi wajen yaki da annobar, hakan bai sanyaya mata gwiwa wajen samar da kayayyakin tallafi ga kasashen Afrika da ma sauran kasashen duniya don yaki da annobar ta COVID-19 ba, duk kuwa da cewa ita kanta tana fama da matsalar annobar.

Ko shakka babu huldar hadin gwiwar moriyar juna dake tsakanin Afrika da Sin za ta kara kyautatuwa a nan gaba.

A halin yanzu, gaba daya adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a kasashen Afirka ya zarce dubu 40, adadin da yake cigaba da karuwa a kai a kai. Rahotanni sun nuna cewa an samu barkewar cutar a kusan daukacin kasashen nahiyar Afrika.

A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, kasar Sin tana samar wa kawayenta dake nahiyar Afirka tallafi gwargwadon karfinta ta hanyoyi daban daban, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin tana son nuna godiya ga 'yan uwanta saboda goyon bayan da suka bata yayin da take fama da wahalar dakile annobar, hakan kuma ya nunawa al'ummun kasa da kasa cewa, kasar Sin tana sauke nauyin dake bisa wuyanta a bangaren kiyaye lafiyar jama'a a fadin duniya.

Hakika kasar Sin tana samarwa kasashen Afirka tallafi domin yaki da annobar ta hanyar daukar hakikanin matakai, wanda yasa ta samu yabo matuka daga manyan jami'an kasashen nahiyar da dama, inda suka bayyana cewa, dadaddiyar zumuntar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka zata jure dukkan jarrabawar da suke fuskantar, kana sassan biyu zasu kafa kyakkyawar makoma yayin da suke kokarin dakile annobar tare.

Shi ma shehun malami a fannin siyasa da dangantakar dake tsakanin kasa da kasa na jami'ar Abuja ta kasar Nijeriya, Agaba Halidu, ya fidda sharhi mai taken "Sin na yaki da cutar numfashi ta COVID-19 cikin himma da kwazo: Mene ne kasashen Afirka zasu iya koya daga wajenta?" a jaridar Leadership ta Nijeirya. Cikin sharhin, ya yabawa kasar Sin kan yadda take sa kaimi ga al'ummomin kasarta, ya kuma jaddada cewa, saboda matakan kandagarki da hana yaduwar annobar da kasar Sin ta dauka yadda ya kamata, ya dace kasashen Afirka su koyi fasahohin Sin wajen yaki da cutar COVID-19.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China