2020-05-14 21:41:33 cri |
Kalaman nasa na zuwa ne, yayin da Amurka ta sanar da cewa, masu satar bayanai ta yanar gizo na kasar Sin sun sace bayanan hukumomin nazarin kwayar cutar COVID-19 na kasar. Zhao ya kara da cewa, kasar Sin tana adawa da matakan Amurka na shafa mata bakin fenti, yana ganin cewa, a daidai lokacin da ake kokarin dakile annobar a fadin duniya, bai dace a kawo batun dora laifin satar bayanai ta yanar gizo ba.(Jamila)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China