Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta kammala kashi na biyu na gwajin alluran rigakafin COVID-19 a Yuli
2020-05-15 19:27:39        cri
Babban jami'i a hukumar lafiya ta kasar Sin Zeng Yixin, ya bayyana cewa, kasar Sin na sa ran kammala kashi na biyu na gwajin alluran rigakafin COVID-19 a farkon watan Yulin.

Da yake karin haske yayin taron manema labarai da hukumar ta kira Jumma'ar nan, ya ce ya zuwa yanzu, ba a samu wasu manyan matsaloli a gwajin farko na alluran rigakafin cutar da aka yi ba.

Daga cikin alluran riga kafin da ake gwajin nasu, sun hada da adenovirus vecrot da wasu alluran guda hudu da hukumar kula da magunguna ta kasar Sin take bin diddiginsu.

Zeng ya ce, masu aikin sa-kai 2,036 ne suka amince a gwada kashi na biyu na alluran rigakafin a jikinsu, kuma masu bincike na tantance ko riga kafin ba shi da hadari yana kuma aiki, ko akasin haka.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China