Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aiktar wajen Sin: Jita-jita kullum jita-jita ne, ko da an maimaita su sau dubu
2020-05-14 21:42:11        cri
Kwanan baya sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya soki gwamnatin kasar Sin cewa, ta ki samar da bayanan dake shafar annobar COVID-19, kan wannan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana yau Alhamis a yayin taron ganawa da manema labarai a nan birnin Beijing cewa, jita-jita kullum jita-jita ne, ko da an maimaita su sau dubu.

Zhao ya kara da cewa, a ranar 12 ga wata, darektan cibiyar CDC ta Amurka Robert Redfield ya halarci taron sauraren ra'ayoyin jama'a da majalisar dattijai ta Amurka ta kira, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ta sanar da bayanai game da bullar cutar huhun da ba a san asalinta ba a birnin Wuhan na lardin Hubei ga hukumar lafiya ta duniya a ranar 31 ga watan Disamban shekarar 2019, daga baya wato a ranar 2 ga watan Janairun bana, cibiyar CDC ta Amurka ta yi cudanya da takwararta ta kasar Sin, inda suka tattauna cikin lumana.

Zhao ya ce, kasar Sin tana fatan Amurka za ta kula da tsaron rayukan al'ummunta, haka kuma ta dauki matakan da suka dace domin rage hasarar rayuka a kasar, a maimakon dora laifi ga wasu.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China