Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata Sin da Afirka su hada kai wajen kafa tsarin aikin noma na zamani
2020-05-26 11:35:51        cri
Tun daga farkon shekarar bana, a sakamakon bala'in fara da cutar COVID-19, an samu manyan hasarori a fannin aikin noma a yankin tsakiya da gabashin nahiyar Afirka, matsalar karancin abinci ta tsananta.

Wakilin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC, kuma mataimakin shugaban kwalejin kimiyyar aikin noma na lardin Anhui Zhao Wanping, ya bayyanawa wakilinmu a kwanakin baya cewa, kasar Sin tana son sa kaimi ga hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afirka, a fannin aikin noma, don taimakawa kasashen Afirka wajen tinkarar matsalar karancin abinci.

Zhao Wanping ya yi nuni da cewa, a 'yan shekarun baya da suka gabata, Sin ta shiga aikin tabbatar da isasshen abinci a duniya, da kafa cibiyoyin koyar da fasahohin aikin noma da dama a nahiyar Afirka, da tura masanan aikin noma da dama zuwa kasashen Afirka, tare da samar da gudummawar hatsi ga nahiyar, matakan da suka taimakawa nahiyar Afirka sosai. Amma idan ana son cimma burin kawar da matsalolin aikin noma na kasashen Afirka daga tushe, to kamata ya yi a samar da fasahohin aikin noma, da samun bunkasuwa, kana a nuna goyon baya ga kamfanonin aikin noma na kasar Sin, da su zuba jari a Afirka a dukkan fannoni, don taimakawa nahiyar kafa tsarin aikin noma na zamani.

Zhao Wanping ya kara da cewa, aikin noma na Sin da na Afirka, suna bukatar juna a fannonin da suke da kwarewa, suna kuma iya yin hadin gwiwa a fannoni daban daban, kuma za su samu kyakkyawar makoma. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China