Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Najeriya: Ba wanda zai lalata dangantakar Afrika da Sin
2020-05-08 13:55:30        cri

Dakta Sherrif Ghali Ibrahim mai nazarin siyasa da dangantakar kasa da kasa na jami'ar Abuja ya wallafa wani bayani a jaridar People's Daily mai taken "Hadin kan Afrika da Sin da yakar COVID-19".

Bayanin ya ce, tun bayan barkewar COVID-19, Sin ke nacewa ga ruhin shawarar "ziri daya da hanya daya" da tunanin kyakkyawar makomar bil Adam ta bai daya, inda ta baiwa dukkan Afrika managartan dabaru da taimako mai dajara. Ban da wannan kuma, gwamnatin kasar Sin da kuma kungiyoyi masu zaman kansu sun baiwa Afrika tallafin jiyya sau da dama, haka kuma masanan jiyya na kasar Sin sun gabatarwa hukumomin kandagarki da dakile cututtuka na Afrika, dabaru da fasahohin yaki da cutar ta Intanet, a wani yunkuri na Sin na yin iyakacin kokarinta wajen taimakawa Afrika kawo karshen cutar tun da wuri.

Bayanin ya kuma ce, kwanan baya, an baza jita-jita a kan Intanet don shafawa kasar Sin bakin fenti da nufin lalata dangantakar bangarorin biyu. Yana mai cewa, kamata jama'a su goge idanunsu don kiyaye dangantakar bangarorin biyu, wadda da wuya aka kafa ta, da tabbatar da hadin kan bangarorin biyu don ya tafi lami lafiya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China