Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Najeriya: Neman kudin diyya daga Sin bisa COVID-19 ya sabawa mutuncin bil Adam
2020-05-08 10:58:40        cri

Jiya Alhamis, masanin cibiyar nazarin zaman lafiya da rikici ta Najeriya dakta Olalekan A. Babatunde ya wallafa wani bayani a jaridar Independent cewa, kwanan baya, Amurka ta nemi kudin diyya daga kasar Sin bisa barkewar cutar COVID-19, matakin da ba kasar Sin kadai ya shafa ba, domin yana da alaka da dukkan bil Adam a duniya. A cewarsa, ba a taba ganin irin wannan bukata a tarihi ba, kana ba za a iya magance wannan cuta ba, sai dai an rike tunanin jin kai.

Bayanin kuma ya nuna cewa, ba a taba neman kudin diyya bisa wata annoba a cikin tarihin bil Adam ba. Kuma Sin ta riga ta yiwa duk duniya bayyani kan asalin cutar, har WHO da dai sauran shahararrun masanan Amurka da Turai sun amince da ita. A hakika dai, Donald Trump na nufin dora laifin jami'iyyarsa kan WHO da kasar Sin, domin burinsa shi ne yin tazarce a zaben da za a yi a bana, da kuma hana bunkasuwar kasar Sin.

Shaidu da dama na nuna cewa, Sin ta dauki matakai mafiya inganci a duk fannoni don hana yaduwar cutar, kuma ta samu nasara. Kamata ya yi Amurka da sauran kasashe su daina zargin kasar Sin, kada su siyasantar da cutar da kuma neman kudin diyya daga kasar Sin. Hanya daya tilo da za a bi a halin yanzu ita ce hadin kai da goyon baya da hakuri da juna. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China