Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta yaba wa tallafin gidauniyar Jack Ma da Alibaba na kayayyakin kiwon lafiya ga Afrika a karo da dama
2020-04-29 11:13:53        cri

Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta yaba wa tallafin gidauniyar attajirin kasar Sin Jack Ma da Alibaba na kayayyakin kiwon lafiya ga kasashen Afrika a karon da dama domin ba su kwarin gwiwar yaki da annobar COVID-19 a nahiyar Afrika.

A sanarwar da John Nkengasong, daraktan cibiyar yaki da cutuka masu yaduwa ta Afrika wato (Africa CDC) ya fitar, ya ce, cibiyar lafiyar mai lura da mambobin kasashen Afrika 55, ta yaba wa aniyar gidauniyar Jack Ma da Alibaba na cigaba da taimkawa Afrika domin ganin bayan annobar ta COVID-19 a Afrika, wanda ya kunshi tallafin kayayyakin aikin lafiya da ake matukar bukata gami da musayar kwarewa wajen yaki da annobar.

A sanarwar da Afrika CDC ta fitar ranar Talata ta ce, a halin yanzu tallafin kiwon lafiyar da gidauniyar Jack Ma take baiwa Afrika ya kai wani matsayi mafi girma, ganin yadda ta hada kai tare da cibiyar Africa CDC waje kira wani taron kara wa juna ilmi ta yanar gizo mai taken "Yaki da annobar COVID-19 bisa kwarewar da kasar Sin ta samu a wannan fannin".

A cewar Nkengasong, hadin gwiwa shi ne babban jigo wajen cimma nasara a yaki da COVID-19. Ya ce a karkashin tsarinsu sun zayyana muhimman batutuwa hudu da suka hada da: hadin kai, hadin gwiwa, yin aiki tare, da kuma musayar bayanai, ya kara da cewa, muddin ba su son ganin Afrika ta zama wata babbar cibiyar annobar a nan gaba, tilas ne su yi hadin gwiwa daga bangarori daban daban a matakan al'ummomin yankuna, da matakin kasa, da matakin nahiyoyi, da kuma matakin kasa da kasa.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China