Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar likitocin kasar Sin ta kira taron fadakarwa kan dabarun yaki da cutar COVID-19 a Cote d'Ivoire
2020-05-07 19:07:03        cri
Rahotanni daga ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Cote d'Ivoire sun ce, tawagar kwararrun likitocin kasar Sin ta kira wani taro, kan dabarun yaki da cutar numfashi ta COVID-19, a cibiyar nazarin harkokin lafiya ta kasar, domin fadakar da jama'ar Cote d'Ivoire kan dabarun kasar Sin na yakar cutar.

Shugaban cibiyar, Mista Joseph Bénié Vroh Bi, ya ce duk da cewa akwai bambancin yanayin da ake ciki a Cote d'Ivoire da kasar Sin, amma Cote d'Ivoire ta koyi yadda kasar Sin take dakile yaduwar cutar, domin aiwatar da shirinta na kandagarkin yaduwar cutar daidai da halin da take ciki, al'amarin da ya zama babbar nasara ga hadin-gwiwar kasashen biyu a fannin lafiya. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China