Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Afrika ta Kudu ya zarce 20,000
2020-05-23 16:16:55        cri
Ministan lafiya na Afrika ta kudu Zweli Mkhize, ya ce jimilar mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a kasar ya kai 20,125 a jiya Juma'a.

Yayin bayanin da yake bayarwa a kullum game da yanayin cutar, Zweli Mkhize, ya ce mutane 988 sun kamu cikin sa'o'i 24, wato daga ranar Alhamis zuwa jiya Juma'a.

Ya kara da cewa, adadin wadanda suka mutu sanadiyyar cutar ya kai 397, wanda ya karu da 28 a kan na ranar Alhamis. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China