Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bukaci masu zuba jari su yi amfani da damarmakin zuba jari a bangaren samar da gidaje a Afrika
2020-05-22 09:43:59        cri

An bayyana zuba jari a bangaren samar da gidaje masu arha a biranen nahiyar Afrika, a matsayin daya daga cikin manyan damarmaki ga masu zuba jari, saboda karuwar jama'a da tsananin bukatar gidaje.

Shugaban kamfanin Shelter Afrique, mai samar da gidaje a Afrika, Andrew Chimphondah, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, ana kaura zuwa biranen Afrika, a wani yanayi da nahiyar ba ta taba gani ba, lamarin da ya sa samar da ingantattun gidaje ya zama kalubale.

Ya ce an yi kiyasin cewa, biranen nahiyar na karuwa da sama da mutane 40,000 a kowacce rana, lamarin da ya kara gibin da ake fuskanta da kusan gidaje miliyan 56.

Ya ce misali, a yankin kudu da hamadar Sahara, an yi kiyasin sama da kaso 60 na mazauna birane na rayuwa ne a wuraren zaman 'yan rabbana ka wadata mu, don haka ake bukatar ingantuwar gidaje.

Ya ce ya kamata masu zuba jari a fadin nahiyar, su yi amfani da damar da ake da shi na karanci kudi a Afrika, domin cike gibin da kuma amfana daga bakata mai tsannai da ake da shi na gidaje masu arha a fadin nahiyar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China