Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan siyasar yammacin duniya dake dora alhaki kan kasar Sin ba su san doka ba
2020-05-25 20:23:00        cri

"Kararrakin da aka kai kasar Sin, ba su da kwararan shaidu ko hujjoji, kana ba a taba ganin irinsu ba a duniya." Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ne ya bayyana haka a gun taron manema labaru na zaman taro na 3 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 ga aka shirya a yammacin jiya Lahadi.

Wannan ita ce kakkausar amsa da kasar Sin ta bayar a fili kan wasannin siyasa da wasu 'yan siyasar yammacin duniya suka tsara na "kai karar Sin" da "dora alhaki kan Sin".

Kamar yadda hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta nuna, cutar COVID-19 na iya bulla a kowane wuri a fadin duniya, ita ma kasar Sin ta tafka hasara sanadiyyar cutar. Domin hana yaduwar annobar a duniya, kasar Sin ta katse hanyar yaduwar cutar a cikin gajeren lokaci, hakan ya hana saurin yaduwar annobar, amma ita kanta sakamakon sadaukarwar da ta yi, ta tafka babbar hasara. Managartan matakan da kasar Sin ta dauka a kan lokaci kan wannan annoba da ma bayanai ba a boye suke ba, wadanda suka iya jure jarrabawa a fannonin lokaci da tarihi. Ikirarin da aka yi na "dora alhaki kan Sin" ba kawai ba shi da tushe ba, tamkar fama rauni ne, matakin da ya sabawa da'a da sanin ya kamata.

Kawo yanzu kwararrun likitoci da masana kimiyya na duniya ba su iya tabbatar da asalin cutar COVID-19 ba. Me ya sa 'yan siyasar Amurka suke daukar matakai kan kasar Sin kawai?

Ban da wannan kuma, "karar" da suka yi ba ta da tushe, tamkar wasan yara ne. Idan wadannan 'yan siyasar Amurka sun ci gaba da "kai kara" kan kasar sin, to tamkar keta dokokin kasa da kasa da na muhimmiyar manufar huldar dake tsakanin kasa da kasa, ciki har da zaman daidai wa daida kan 'yanci da hurumin kasa da dai sauransu. (Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China