Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan siyasar Amurka dake nufin tayar da wariyar launin fata na kokarin yada gaba a al'ummar kasar
2020-05-24 23:24:56        cri

 

"Yanzu ina fuskantar hadarin lafiya a yayin da nake ceton rayuka, amma na gamu da wulakanci sakamakon launin fuskata." Lucy Li, likita ce 'yar asalin kasar Sin wadda ke aiki a sashen alluran barci na babban asibitin Massachusetts ta fadi haka ne cikin bakin ciki. Kwanan baya, jaridar Washington Post ta kasar Amurka ta bada labari cewa, a farkon lokacin da aka samu bullar cutar COVID-19 a kasar, wani namiji ya ci zarafin Lucy Li a kan haryarta ta koma gida. Ban da wannan kuma, a yayin da take aiki, wasu da suka kamu da cutar su ma sun ki yarda da samun jinya daga wajenta saboda ita 'yar asalin kasar Sin ce.

A yayin da suke kokarin ceton mutane duk da cewa suna fuskantar hadarin kamuwa da cutar, a sa'i daya kuma suna fuskantar matsin lamba a fannonin wariyar launin fata da kyamar baki. Yanzu dai masu aikin jinya 'yan asalin kasar Sin dake Amurka, ciki har da Lucy Li suna cikin wani mawuyacin hali da ba a taba ganin irinsa ba, game da haka, kafofin watsa labaru na Amurka sun ce, "ana wata ga wata".

 

Farfadowar wariyar launin fata da ake samu a yanzu haka a kasar Amurka, tana da nasaba da hura wuta da 'yan siyasar kasar suka yi. Tun bayan bullar cutar a kasar, domin boye hasarar da suka yi wajen yakar cutar, wasu 'yan siyasar kasar suna ta neman shafawa kasar Sin kashin kaji, da nemo moriya a fannin siyasa ta hanyar bata sunan kasar Sin, don kawar da hankalin al'umma kan yadda suka yi sakaci da aikinsu wajen dakile cutar.

 

Sakamakon haka, wasu Amurkawa, ciki har da 'yan asalin Asiya, Afirka da Latin Amurka da dai sauransu suna fuskantar kalubale a fannoni masu yawa. Ga misali, sakamakon sakaci da aiki wajen yakar annobar, suna gamuwa da matsala kan rayuwarsu da lafiyarsu, a waje daya kuma, yaduwar annobar ta sanya su rasa aikin yi, hakan halin tattalin arzikinsu ya durkushe. Bisa kididdigar da sashen kwadago na jihar New York ya yi, an nuna cewa, a cikin makwanni 6 wato tun bayan bullar cutar har zuwa ranar 9 ga watan Mayu, Amurkawa 'yan asalin Asiya sama da dubu 195 a karon farko sun gabatar da rokon rasa aikin yi, adadin da ya ninka sau 56 bisa na makamancin lokacin bara.

 

 

Abin da ya fi tsanani shi ne, 'yan asalin Asiya da Afirka suna ma fuskantar wariyar launin fata. Bisa binciken da aka yi a duk al'ummar kasar a watan Afrilun bana, an nuna cewa, bayan bullar annobar, Amurkawa 'yan asalin Asiya da yawansu ya kai kashi 60 cikin 100 sun taba ganin kalubale ko tashin hankali da aka kai musu.

Cuta ba ta san kasa ba kuma ba ta san launin fata ba, sai dai an hada kai da nuna kyautatawa ga juna za a iya cimma nasarar yakar cutar. (Mai fassara: Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China