Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Margaret Chan Fung Fu-chun: za a kwashe tsawon lokaci kafin shawo kan COVID-19 ta amfani da kimiyya da fasaha
2020-05-25 13:00:26        cri

Yayin da zama karo na biyu a zango na 3, na majalissar ba da shawara kan harkokin jama'ar kasar Sin ta 13 ke ci gaba da gudana a nan birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, mambar majalissar ta CPPCC Margaret Chan Fung Fu-chun, wadda kuma a baya ta taba rike mukamin babbar daraktar hukumar lafiya ta duniya WHO, ta bayyana mahangarta game da tasirin hadin gwiwar kasa da kasa a yakin da ake yi da wannan annoba, da ma batun gina al'umma mai makomar bai daya ga daukacin bil Adama.

Chan Fung Fu-chun ta kara da cewa, har yanzu ba a kai ga gane hakikanin yanayin wannan cuta ta COVID-19 ba, yayin da ake ci gaba da yunkurin samar da magunguna da rigakafin ta. Kuma za a shafe tsawon lokaci kafin a kai ga ganin bayan ta, karkashin dabaru na kimiyya da fasaha. Bugu da kari, halayyar zaman jira na dirshan, da yin wasarairai da matakan dakile ta, na iya haifar da mummunan sakamako da ba za a iya gyara shi ba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China