Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin tana fatan ganin hadin gwiwa tsakanin masanan Sin, Amurka, da Afirka a fannin yakar COVID-19
2020-05-18 20:17:55        cri
A yau Litinin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya furta cewa, hadin gwiwa yana da muhimmanci sosai, a aikin dakile cutar COVID-19 a duniya. Don haka kasar Sin ke nuna cikakken goyon baya ga masanan kasar, da takwarorinsu na kasar Amurka, da kuma na kasashen Afirka, domin su kara tattaunawa kan batun hadin gwiwa a fannin yakar cutar COVID-19.

Kwanakin baya, cibiyar nazarin huldar kasa da kasa ta zamani ta kasar Sin, da cibiyar nazari ta Carter ta kasar Amurka, gami da cibiyar nazarin al'amuran kasa da kasa ta kasar Afirka ta Kudu, sun yi hadin gwiwa wajen shirya wani taron karawa juna sani, dangane da aikin hadin gwiwar da ake yi don dakile cutar COVID-19, inda aka tattauna yadda za a yi hadin kai tsakanin bangarorin Sin, Amurka, da kuma kasashen Afirka. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China