Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin tana maraba da yadda aka zartas da kudurin tinkarar cutar COVID-19
2020-05-20 20:06:45        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijiang, ya furta a yau Laraba cewa, kasar Sin tana maraba da yadda bangarori masu halartar taron harkar lafiya na duniya karo na 73, suka cimma matsaya, tare da zartas da wani kuduri game da aikin dakile cutar COVID-19 a duniya a jiya Talata.

Zhao ya ce, cikin wannan kuduri, an nuna amincewa da goyon baya ga muhimmiyar rawar da hukumar lafiya ta duniya WHO ke takawa, tare da yin kira ga kasashe mambobin hukumar, da su kauracewa nuna bambanci ga wasu kasashe da al'ummu, da watsi da matakin shafa wa wani bangare bakin fenti. Sauran matakan sun kunshi kokarin kawar da bayanan jabu, da na kuskure, gami da kara hadin gwiwa a fannonin samar da na'urorin gwaje-gwajen kwayoyin cuta, da dabarun jinya, da magunguna, da allurar rigakafin cuta, da dai makamantansu.

A cewar Zhao, duk wadannan fannoni sun dace da ra'ayin kasar Sin, kuma sun kasance buri na bai daya na galibin kasashen duniya. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China