Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakakin Sin: Amurka ta san wane ne ke kokarin yada bayanai na jabu
2020-05-19 20:39:38        cri
Don gane da yadda wasu jami'an kasar Amurka ke zargin kasar Sin da kokarin " yada bayanai na jabu", kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin , Mista Zhao Lijian, ya furta a yau Talata cewa, wannan zargi ba shi da tushe ko kadan. Sa'an nan kuma game da ainihin wane ne ke kokarin yada jita-jita, wannan tambaya a cewar sa kasar Amurka ta san amsarta, kana mutanen duniya su ma sun san hakan sosai.

Kafin haka, wani jami'in cibiyar mu'amala da kasashe daban daban karkashin majalisar gudanarwar kasar Amurka, Lea Gabrielle, ya ce gwamnatin kasar Sin na yin amfani da wasu sabbin kafofin watsa labaru, irin su manhajar sada zumunta ta Twitter, wajen yada bayanai na jabu masu alaka da yanayin annobar COVID-19.

A cewarsa, kasar Sin ta yi amfani da wasu fasahohi wajen kara yada bayanai, kana a kwanakin nan, an samu karin wasu shafuka na Twitter mallakar jami'an diplomasiyar kasar Sin.

Game da wannan batu, mista Zhao Lijian ya ce, kamfanin Twitter ya riga ya mayar da martani, inda ya ce binciken da aka yi kan shahufan ya nuna cewa, maganar da kasar Amurka ta yi ba shi da tushe.

Zhao ya kara da cewa, hakika wasu 'yan siyasa na kasar Amurka ne suke ta kokarin neman dora wa kasar Sin laifin haddasa barkewar cutar COVID-19 a duniya, suna kara shafawa kasar Sin bakin fenti, tare da kokarin yada jita-jita. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China