Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta nuna adawa da doka kan COVID-19 da 'dan majalisar dattawan Amurka ya gabatar
2020-05-13 21:09:36        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana adawar kasarsa kan wata doka da ta shafi COVID-19 da 'dan majalisar dattawan Amurka Lindsey Graham ya gabatar, dokar da za ta baiwa shugaba Donald Trump na Amurka ikon kakabawa kasar Sin takunkumi, idan har kasar Sin din ta ki ba da hadin kai, da ma ba da bayanai kan abubuwan da suka kai ga barkewar cutar COVID-19.

Zhao ya ce, dokar tamkar yin fatali ne da shaidu. Rashin hankali ne kuma kokari ne na dorawa kasar Sin laifin yaduwar cutar a kasar. Ya ce, har kullum kasar Sin tana gudanar da aikin yaki da COVID-19 a bayyane, tana kuma aiki kafada da kafada da WHO. Kuma duniya ta ga yadda irin gudummawar da kasar Sin ta bayar wajen hana yaduwar wannan annoba.

Ya kara da cewa, "Babu wata kasuwar sayar da dabbobin daji" da ake batu a kai a kasar Sin. Yana mai cewa, kasar Sin ta kafa dokar haramta farauta, ciniki da safara ko cin namun daji.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China