Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya bukaci a nazarci tattalin arzikin kasar bisa mahanga mai dogora zango da basira
2020-05-23 20:47:28        cri
Shugaba Xi Jinping ya jaddada bukatar nazartar yanayin tattalin arzikin kasar bisa mahanga mai cin dogon zango da ya shafi dukkan bangarori, kuma bisa basira. Yana mai bukatar a samar da sabbin damarmaki yayin da ake fama da kalubale tare da samar da sabbin dabaru yayin da ake fuskantar sauye-sauye.

Xi Jinping wanda kuma shi ne sakatare-janar na kwamitin tsakiya na JKS kuma shugaban rundunar sojin kasar, ya bayyana haka ne lokacin ya halarci zaman hadaka na 'yan majalisa masu bada shawara kan harkokin siyasa dake kula da harkokin tattalin arziki. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China